7 Yuli 2021 - 14:09
​Iran: Mun Riga Mun Sanar Da IAEA Kan Shirinmu Na Tace Uranium Kashi 20% U-235

Iran ta bayyana cewa ta riga ta sanar da hukumar makamashin nukiliya ta duniya kan shirinta na tace sanadarin uranium.

ABNA24 : Wakilin Iran a hukumar makamshin nukiliya ta duniya Kazem Garib Abadi ya bayyana cewa, sun sanar da hukumar IAEA cewa za su fara shirin tace sanadarin uranium kashi 20% a mataki na U-235.

Gharib Abadi ya ce, wannan da can yana daga cikin tsare-tsaren kasar a cikin shirinta na nukiliya, wanda hukumar IAEA ta san da hakan, saboda haka Iran za ta ci gaba da aiwatar da shirinta nata kamar yadda ta tsara ba tare da wani jinkiri ba.

Sai dai a nata bangaren hukumar makamashin nukiliya ta duniya ta bayar da wani rahoto a jiya Talata dangane da niyar Iran ta aiwatar da shirin tace karfen uranium kashi 20% U-235, inda hukumar ta nuna damuwa matuka kan hakan.

Ita ma a nata bangaren gwamnatin Amurka ta fitar da bayani da ke bayyana yunkurin na Iran da cewa zai mayar da hannun agogo baya a tattaunawar da ake yi kan shirinta na nukiliya, domin kuwa matakin na Iran yana a matsayin wata babbar barazana.

Tuni dai ta bayyana cewa za ta ci gaba da daukar matakan da ta ga sun dace daidai da maslaharta dangane da shirin nata na nukiliya, sakamakon kasa cika alkawulla daga bangaren wasu kasashe da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar shirin nata.

342/